in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya jaddada karfafa huldar dake tsakanin Sin da Rasha
2017-11-01 19:34:14 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya nanata kudurin kasarsa na kara zurfafa alakar dake tsakaninta da kasar Rasha.

Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a yau Laraba yayin ganawarsa da firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev a nan birnin Beijing, ya ce a shirya kasar Sin take ta kara fadada hadin gwiwa da Rasha a fannoni daban-daban, da kara hada kai a harkokin kasa da kasa da kuma gina al'umma mai kyakkyawar makoma.

Xi ya bayyana imanin cewa, hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu, za ta samar da sabbin damammaki da kyawawan sakamako. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China