Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya umarci gwamnatinsa ta shirya rahoto kan irin kokarin da take na yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.
Kamfanin dillancin labarai na MENA ya ruwaito cewa, Abdel-Fattah Al-Sisi ya bada umarnin ne a jiya Alhamis, lokacin da yake ganawa da firaministan kasar da kuma wasu ministoci a birnin Alkahira.
Shugaban ya bukaci a yi nazarin binciken da wasu ma'aikatu mabambanta suka yi a baya, domin mika su ga majalisar koli na yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi don taimakawa sabuwar majalisar da aka kafa wajen samar da ingantaccen tsarin yaki da ta'addanci. (Fa'iza Mustapha)