Bisa labarin da aka bayar, an ce, a yayin babban taron MDD karo na 71 da aka rufe a kwanan baya, an zartas da wani kuduri, inda aka rubuta "ka'idojin tattaunawa tare, da neman ci gaba tare, da kuma cin gajiya tare" wanda bangaren Sin ya gabatar.
Game da wannan mataki, Mr. Geng Shuang ya bayyana cewa, a matsayin kasar da tattalin arzikinta ke samun ci gaba, kuma daya daga cikin kasashe maso tasowa, bangaren Sin yana fatan yin hadin gwiwa da al'ummomin kasashen duniya duka, wajen gudanar da gyare-gyare ga tsarin daidaita harkokin kasa da kasa, bisa ka'idoji da tunanin da aka ambato a baya, ta yadda za a iya kara sanin sauye-sauye a halin da ake ciki a duk duniya, da kuma taimakawa kasashen duniya gaba daya yadda ya kamata. (Sanusi Chen)