A cewar mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan kasar, wadanda ake zargin sun hada da 'yan asalin kasar Saudiyyan 32, da 'yan kasashen waje 14 da suka hada da kasashen Pakistan, Yemen, Afghanistan, Masar, Jordan da kasar Sudan, kuma tuni aka tsare mutanen a yammacin birnin Jeddah.
Jami'in ya ce ana zargin mutanen da hannu wajen kitsa harin ta'addanci wanda aka kaddamar kan masu ibada a masallacin manzon Allah S.A.W a shekarar data gabata.
Ya kara da cewa, ana zargin mutanen da kaddamar da harin ta'addanci a wani yanki na asibitin Suleiman Fakih dake Jeddah a shekarar bara.(Ahmad Fagam)