in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin Najeriya: An kashe matar shugaban Boko Haram a hare hare ta sama
2017-10-26 10:06:09 cri
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da cewa, an hallaka matar jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a wasu hare-hare ta jiragen yaki da sojojin saman suka kaddamar a ranar Laraba.

Mai magana da yawun rundunar sojin saman kasar Olatokunbo Adesanya, yace wasu bayanan sirri sun nuna cewa an kashe Malama Firdausi Shekau, uwar gidan Abubakar Shekau, wanda aka yi amanna shine shugaban kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram.

Kakakin rundunar ya ce, an kashe matar ne a lokacin da ta wakilci mijinta a yayin wani taro da aka shirya na mambobin kungiyar 'yan ta'adda a ranar 19 ga watan Oktoba a wani waje inda sojojin saman Najeriyar suka yi musu lugudan wuta.

Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa harin da aka kai daga sama ya haddasa gobara, wadda ta yi mummunar barna ga maboyar 'yan ta'addan.

Kakakin ya kara da cewa, hare hare ta saman ya kashe mafi yawan 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram a wannan yankin.

Dakarun Najeriya suna samun galaba a yakin da suke yi da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram, inda suka yi nasarar fatattakar mayakan daga babbar maboyarsu dake dajin Sambisa, wajen da ya kasance a matsayin sansani mafi girma na horas da 'yan ta'addan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China