in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara kama wani dan Boko Haram a yankin kudu maso yammacin Najeriya
2017-10-04 12:07:06 cri
Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta ce, ta yi nasarar damke wani da ake zaton dan kungiyar Boko Haram ne mai shekaru 20 da haihuwa dan asalin jihar Nasarawa dake yankin tsakiyar kasar ta Najeriya. Kuma a halin yanzu ta mika shi a hannun sojoji domin gudanar da Karin binkice da sauran matakan da suka dace.

Kamen na ranar Lahadi ya biyo bayan kama wani mutum mai shekaru 42 da shi ma ake zargin dan kungiyar ta Boko Haram ce da jami'an tsaron suka yi a ranar 25 ga watan Satumba a yankin karamar hukumar Isua-Akoko dake jihar ta Ondo.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Ondo Gbenga Adeyanju ya ce, an kama dukkan mutanen da ake zargi ne a wuri guda. A cewarsa, wanda ake zargin ya ce abokinsa ne ya yi masa tayin shiga kungiyar shekaru biyu da suka gabata.

Bugu da kari, mutumin da ake zargin ya amsa cewa, ya kashe mutane biyu kafin a kai ga kama shi, sannan shi da dan uwansa suna shirin kai harin ta'addanci a jihar ta Ondo a lokacin da jami'an tsaro suka yi nasarar damke shi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China