Yayin wani dandalin tattaunawa kan raya sana'ar yawon bude ido wanda aka yi jiya Jumma'a a birnin Dar es Salaam, Mihayo ya ce, sana'ar yawon shakatawa na daya daga cikin muhimman sana'o'in Tanzaniya. Yayin da layin dogo da ya hada Tanzaniya da Zambiya ke taimakawa ci gaban sana'ar yawon bude ido a Tanzaniya, ana fatan kara samun Sinawa da za su je yawon shakatawa kasar. Mihayo ya kuma yi imanin cewa, irin kyakkyawan muhallin namun daji gami da wuraren shakatawa na bakin teku dake Tanzaniya, za su burge Sinawa.
Shi ma a nata bangaren, jakadar kasar Sin dake Tanzaniya, Wang Ke ta yi imanin cewa, sakamakon kokarin da Sin da Tanzaniya suka yi, na kara tallata wuraren yawon shakatawa na Tanzaniya, tana mai cewa za'a kara samun masu yawon shakatawa daga kasar Sin. (Murtala Zhang)