in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Tanzaniya ya kori babban darektan TANESA
2017-01-02 12:14:13 cri
Shugaba John Magufuli na kasar Tanzaniya ya kori manajan darektan hukumar samar da wutar lantarki ta kasar (TANESA) Felchesmi Mramba, bayan da hukumar ta yi karin sama da kaso 80 cikin 100 na kudin wuta.

Gabanin tsige Mramba, shugaba Magufuli ya shaidawa taron mabiya addinin kirista a wata majami'a da ke yankin Kagera cewa, karin kudin wutan da hukumar ta yi zai kawo koma baya ga shirin da kasar take yi na farfado da masana'antunta.

Wata sanarwar da sashen watsa labarai na fadar shugaban kasar ya rabawa manema labarai ta bayyana cewa, shugaba Magufuli ya nada Tito Mwinuka domin maye gurbin Mramba a matsayin manajan darektan hukumar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China