in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya ta yabawa Sin game da haramta safarar hauren giwa
2017-01-15 13:13:57 cri

Tsohon shugaban kasar Tanzaniya Benjamin Mkapa a jiya Asabar ya yabawa kasar Sin sakamakon haramta fataucin hauren giwa, kana ya bukaci sauran kasashen duniya da su yi koyi.

Ya ce haramta safarar hauren giwar da kasar Sin ta yi zai taimaka wajen kawo karshen farautar giwaye a Tanzaniya.

Mkapa ya yi wannan yabo ne bayan kammala wani tattaki da zummar wayar da kan jama'a game muhimmancin adada gandun daji da kuma bukatar da ake da shi ga al'umma su shiga shirin yaki da farautar giwaye.

Ya ce abu mafi muhimmanci shi ne hana masu farautar giwayen damar yin cinikayyar hauren giwa a duniya baki daya.

Shi dai wannan tattakin an gudanar da shi ne na tsawon kilomita 5 daga ofishin jakadancin kasar Sin zuwa otel din sea cliff, wanda ofishin jakadancin kasar Sin dake Tanzaniya ya shirya, ya samu halartar mutane sama da 600, ciki har da manyan jami'an gwamnati, da kungiyoyi masu zaman kansu, da masanan harkokin gandun daji, da kuma jami'an diplomasiyya.

Mkapa ya ce, ya kamata kasashen duniya su yi koyi da kasar Sin, domin ceto rayuwar giwaye domin gudun bacewarsu daga doron kasa, wadanda tuni sun riga sun bace a wasu kasashen duniya.

Ya kara da cewa, lasar Sin ba ita ce kadai ke yin safarar hauren giwaye ba, akwai kasashe masu yawa a yankin Turai, da Amurka da yankin gabas mai nisa, ya ce ya kamata kasashen su dauki matakan haramta safarar hauren giwayen domin samun nasarar wannan shirin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China