in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Tanzaniya ta magance kura-kuran da APRM ya gano game da kasar
2017-07-20 10:15:03 cri

Mahukuntan kasar Tanzaniya sun bayyana cewa, sun fara daukar matakan da suka wajaba don magance irin kura-kuran da shirin APRM ya gano game da kasar.

Manufar shirin na APRM wanda kasashen nahiyar suka cimma a tsakaninsu ita ce tabbatar da cewa, al'amura na gudana yadda ya kamata a fannoni siyasa, tattalin arziki da tafiyar da harkokin mulki bisa doka, ka'idoji da kiyaye ingancin kayayyaki tsakanin kasashen Afirka.

A jawabinta yayin kaddamar da rahoton shiri na kasar, mataimakiyar shugaban kasar Tanzaniya Samia Hassan Suluhu, ta bayyana cewa, shirin APRM ya taimaka wajen dorewar tsarin demokiradiya da kuma yadda ake damawa da 'yan kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China