Cikin sakonsa, Xi Jinping a madadin gwamnati da al'ummar kasar Sin, ya jajantawa wadanda iftila'in ya rutsa da su tare da iyalansu.
Da sanyin safiyar Litinin da ta gabata ne gefen wani tsauni ya ruguje yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya, abun da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 300 tare da raba wasu sama da 2,000 da muhallansu a wajen Freetown, babban birnin kasar Saliyo. (Fa'iza Mustapha)