Wata sanarwa da shirin ya fitar a jiya Asabar, ta ce 'yan sandan da suka fito daga Kenya da Uganda da Zambia da Nijeriya za su kasance a Somalia tsawon shekara guda suna rangadin aiki, inda za su horar da takwarorinsu na Somalia yadda za su yi hulda da al'umma wajen tabbatar da tsaro.
Da yake kaddamar da horon, kwamishinan 'yan sandan shirin AMISOM Brig-Janar Anand Pillay, ya shaidawa jami'an cewa, shirin na da ka'idojin aiki kuma zai ba kowanne daga cikin su kwafinsa, domin su fahimci abun da ake bukata daga gare su ta fuskar ladabi da biyayya da yanayin aiki da kuma yadda za su yi hulda a tsakaninsu da kuma al'ummar Somalia.
Horon zai shafi wasu maudu'i da suka hada da kare cin zarafin mata yayin rikici da kare yara da bada agajin jin kai da tsaron al'umma da kuma kare hakkokin bil'adama da tsarin al'adu.
Kwamishinan ya kuma bukaci jami'an su kasance masu ladabi da biyayya a ko da yaushe tare da yin aiki tukuru domin ba da gudunmuwa wajen farfado da Somalia. (Fa'iza Mustapha)