Kakakin birnin Mogadishu na kasar Somalia Abditifitah Halane, ya shaidawa manema labarai cewa, bam din dake cikin motar ya fashe ne a kusa da wata motar haya a kasuwar Hamarweyne.
Abditifitah Halane wanda ya ce mutane 7 ne suka mutu sanadiyyar harin, ya ce wadanda harin ya rutsa da su na cikin motar hayar ne a lokacin da bam din ya fashe.
Kawo yanzu dai, babu wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin harin na baya-bayan nan da aka kai kasar dake kahon Afrika. (Fa'iza Mustapha)