in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari kan fararen hular Syria a yayin da suke tserewa daga yankin dake karkashin ikon kungiyar IS
2017-08-31 10:42:49 cri
Rahotanni daga kasar Syria na cewa, a jiya Laraba ne, aka kaiwa wata motar dake dauke da fararen hular kasar Syria hari da bama-bamai, yayin da suke kokarin tserewa daga birnin Bukamal na lardin Deir ez-Zor dake karkashin ikon kungiyar IS zuwa lardin Hasakah dake arewa maso gabashin kasar Syria. Harin ya haddasa rasuwar mutane guda 10, yayin da mutane guda 28 suka jikkata, kuma a halin yanzu, ana yi musu jinya a wani asibitin dake lardin Hasakah.

A kwanan baya ne dai, sojojin gwamnatin kasar Syria suka samu nasarori da dama a yakin da suke fafatawa da kungiyar IS, inda suka kwace iko yankuna da dama dake hannun mayakan.

Burin sojojin gwamnatin kasar Syria na gaba shi ne, kwace iko a lardin Deir ez-Zor, wanda a halin yanzu, yake hannun kungiyar ta IS. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China