Gao Feng ya bayyana haka ne a jiya yayin wani taron manema labarai, inda ya ce, kawo yanzu, kamfanonin kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen gina yankunan hadin-gwiwar cinikayya da kasuwanci a wasu kasashe 24, lamarin da ya samar da dimbin guraban ayyukan yi.
Har wa yau, Gao ya ce, ana nan ana gaggauta gudanar da wasu muhimman ayyukan hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen dake cikin shawarar 'ziri daya da hanya daya'. A nan gaba ma, ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da nasarorin da aka samu a wajen babban dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar 'ziri daya da hanya daya', da kara musayar ra'ayi da kasashen dake cikin shawarar, a wani kokari na habaka tattalin arzikin duniya baki daya.(Murtala Zhang)