Shirin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta martaba tunanin yin hadin gwiwa cikin lumana, da bude kofa da yin hakuri, da musayar fasahohi, da neman samun ci gaba da cin moriyar tare da ka'idar amincewa da juna daga manyan fannoni da jingine bambanci dake tsakanin juna, da bude kofa domin yin hadin gwiwa, da raya kasuwanni, da samun ci gaba tare da sauransu, domin sa kaimi ga tabbatar da shirin neman samun dauwamammen ci gaba a yankin teku da MDD ta tsara nan da shekarar 2030, ta yadda za a yi hadin gwiwa a fannoni daban daban a yankin teku tare da kasashen dake hanyar siliki ta yankin teku ta ratsa, da kokarin kulla dangantakar abokantaka ta samun moriyar juna, da bulo da harkokin cinikayya maras gurbata muhalli, ta yadda za a samu dauwamammen ci gaba.(Fatima)