in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen dake cikin shawarar 'ziri daya da hanya daya' za su hada hannu wajen yaki da lalacewar dazuka
2017-09-11 10:36:09 cri

Kasashen dake cikin shawarar 'ziri daya da hanya daya' sun kaddamar da wani aikin hadin gwiwa na yaki da kwararar hamada.

An kafa tsarin ne a wani bangare na taron kasashen da suka cimma yarjejeniyar yaki da kwararar hamada na 13, na babban taron MDD kan yaki da kwararar hamada (UNCCD).

A cewar shugaban hukumar kula da dazuka ta kasar Sin Zhang Jianlong, tsarin zai taimakawa kasashen da suka hada gwiwar wajen samar da kudade da musayar bayanai da ba da horo da daukar darasi daga juna daga ayyukan da suka aiwatar.

Zhang Jianlong ya ce, yunkurin zai ba da gudummuwa ga shirin kare lalacewar filaye da kuma muradun ci gaba da MDD ke son cimmawa daga nan zuwa shekarar 2030.

Ita ma wata jami'ar hukumar Pan Yingzhen, ta ce tsarin zai samar da kudade ta hanyar kafa asusu da ba da gudumuwa da kuma hadin gwiwa tsakanin bangarori masu zaman kansu da na gwamnati da sauransu.

A bara ne kasar Sin da babban taron MDD kan yaki da kwararar hamada UNCCD suka kaddamar da wani shirin hadin gwiwa domin yaki da kwararar hamada da farfado da yankunan da suka lalace wadanda ke kan hanyar ziri daya da hanya daya. Yunkurin zai shafi yankin nahiyar Turai da Asiya da ya hada kasar Sin da Gabas ta Tsakiya da Turai da nahiyar Afrika, wadanda ke kan tsohuwar hanyar siliki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China