Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Gaoli ya yi kira ga mahukuntan kasar Sin da su gina shawarar "Ziri daya da hanya daya" cikin lumana, makoma mai kyau da buge kofa da gudanar da kirkire-kirkire gami da yadda za a hade wayewar kan kasashe.
Zhang Gaoli wanda ya bayyana hakan a yau Jumma'a lokacin da yake jawabi a taron aikin game da shawarar "Ziri daya da hanya daya". Ya ce, wajibi ne kananan hukumomi su aiwatar da manufar shawarar ta wanzar da zaman lafiya da yin hadin gwiwa, bude kofa da damawa da kowa da kowa, koyo da juna da cin moriyar juna, ta yadda za a cimma nasarorin da ake fata daga shawarar da kasar Sin ta gabatar da ita.
Ya kara da cewa, akwai bukatar kasar Sin ta hade matakan ci gaban kasashen da shawarar ta tsara ta cikinsu tare da kara karfafa matakan tsaron kasashen katare na gina hanya mai cikakken tsaro. (Ibrahim)