Yayin taron, Mista Qu Weizhi, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar masu sana'ar sadarwa ta zamani ta kasar Sin, ya ce kasar Sin za ta habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen da suka shiga shirin "Ziri daya da Hanya daya" a fannin amfani da yanar gizo ta Internet, da raya fasahohin sadarwa. Haka zalika, za su bude sabon dandali na raya masana'antu, da kafa wani tsari da daidaita ra'ayinsu, don samar da hidima mai inganci.(Bello Wang)