Bangarorin biyu sun sake cimma matsaya daya kan wasu ka'idojin da za su bi, ciki har da kawar da dukkanin makaman nukiliya a zirin Koriya, da warware matsalar makaman nukiliya na Koriya ta Arewa cikin lumana.
Har wa yau, bangaren Koriya ta Kudu ya kara fahimtar matsayin gwamnatin kasar Sin kan batun girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami sanfurin THAAD, inda ya tabbatar da cewa, girke wadannan na'urorin a Koriya ta Kudu ba ya da nufin kawo barazana ga wasu kasashe, wato ba zai yi illa ga harkokin tsaro na kasar Sin ba. Ita ma kasar Sin ta sake nanata kin amincewarta game da girke wadannan na'urorin THAAD a Koriya ta Kudu.(Murtala Zhang)