Jami'an diplomasiyya daga kasashe fiye da 150 guda fiye da 260 ciki har da jakadun kasashen waje dake kasar Sin ko mukaddashin jakadun fiye da 90 sun halarci taron.
Jami'an sun bayyana cewa, babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 yana da babbar ma'ana, inda aka gabatar da tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, tare da wasu manyan matakan da suka dace da yanayin kasar Sin, wadanda suke nufin makomar bunkasuwar kasar ta Sin, tare da yin babban tasiri ga samun zaman lafiya da wadata da bunkasuwa a duniya gaba daya. (Zainab)