in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin wakilian JKS na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar sun kira taron koyon ka'idojin cikakken zaman taron JKS karo na 19
2017-10-29 13:29:25 cri
A ranar 26 ga wata, kungiyar wakilan JKS na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 ta kira taro domin kara sani game da ka'idojin cikakken zaman taron JKS karo na 19. Shugaban zaunannen kwamitin majalisar Zhang Dejiang ya bada jagoranci kan taron, inda ya kuma ba da jawabi cewa, ya kamata a dukufa wajen koyon ka'idojin da abin ya shafa, musamman ma game da yadda za a aiwatar da tsarin gurguzu bisa jagorancin shugaba Xi Jinping, da kuma tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, da nuna girmamawa ga jama'ar kasar da kuma gudanar da harkokin kasar bisa dokoki, ta yadda za a cimma burin gina zaman jama'ar kasa mai wadata da kuma samun farfadowar kasa baki daya.

A sa'i daya kuma, kungiyar wakilan JKS ta kwamitin majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta kira taro a ranar 26 ga wata, inda shugaban majalisar Yu Zhensheng ya ba da jagoranci kan taron.

An bayyana cewa, ana goyon bayan kudurorin da aka zartas da su a cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19, da kuma rahoton da Xi Jinping ya bayar a madadin kwamitin tsakiya karo na 18. A nan gaba kuma, za ta ci gaba da nuna goyon baya ga sabbin shugabannin da aka zaba a yayin taron wakilan JKS karo na 19. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China