in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu shugabannin kasashe da jam'iyyun Afirka sun taya Xi Jinping murnar kara zama babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS
2017-10-28 13:50:56 cri
Wasu shugabannin kasashe da jam'iyyun Afirka, sun aikewa da wasika, don taya shugaba Xi Jinping murnar zama babban sakataren kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 2.

A jiya Jumma'a ne, Ministar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu Maite Nkoana-Mashabane, ta gana da jakadan Sin dake kasarta Lin Songtian, inda ta isar da sakon murnar da shugaban kasar kuma shugaban jam'iyyar ANC Jacob Zuma ya aikewa Xi Jinping, bisa sake zama babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS a karo na 2. Mashabane ta bayyana cewa, bisa kulawa da goyon bayan da Xi Jinping da Zuma suka nuna, an raya dangantakar dake tsakanin Afirka ta Kudu da kasar Sin cikin sauri, tana mai cewa an gamsu sosai da nasarorin da aka samu yayin raya dangantakar, da kuma imani samun kyakyyawar makoma a nan gaba.

Shi ma Shugaban jam'iyyar Zanu PF na kasar Zimbabwe kuma shugaban kasar Robert Mugabe, ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, Xi Jinping ya sake zama babban sakataren jam'iyyar ne saboda kwarewarsa wajen jagorantar jam'iyyar. Ya ce a karkashin jagorancinsa, kasar Sin tana kulawa da ci gaban kasashen Afirka da samar da gudummawa ga bunkasar nahiyar a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma da sauransu, yana mai bayyana godiya game da wannan.

A nasa bangaren, Shugaban jam'iyyar demokuradiyya ta kasar Gabon kuma shugaban kasar Ali-Ben Bongo Ondima, ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, ya ji dadin ganin Xi Jinping ya sake zama babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma a madadin jam'iyyarsa ta kasar Gabon, yana taya Xi Jinping murna da fatan samun sabbin nasarori yayin da yake kokarin cimma burin kasar Sin a karkashin jagorancinsa.

Shugaban kwamitin kungiyar AU a wannan karo kuma shugaban kasar Guinea Alpha Conde, ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, an sanya tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulkin na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki a cikin kundin tsarin jam'iyyar kwaminis ta Sin, inda ya ce wannan ya bayyana muhimmiyar rawar da Xi Jinping yake takawa yayin da ake kokarin raya kasar Sin, da sa kaimi ga bunkasar kasar da samar da hadin kai da zaman lafiya da wadata a duniya baki daya.

Cikin wasikarta, Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf, ta ce, sanya tunanin shugaba Xi Jinping cikin kundin tsarin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya shaida amincewar da aka yi masa a kokarin da yake na raya kasa karkashin jagorancinsa. Tana mai fatan samun karin nasarori ga jama'ar kasar Sin karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping. (Zainab)

Shi ma Shugaban jam'iyyar demokuradiyya da samun 'yancin kai na kasar Sao tome and Principe kuma Firaministan gwamnatin kasar Patrice Trovoada, ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, sake zama babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta Sin da Xi Jinping ya yi da kuma zartas da kudurori yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, ya tabbatar da cewa, al'ummar kasar Sin sun amince da shugaba Xi Jinping da ya bada gudummawa sosai ga muradunsu, har ma kasa da kasa gaba daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China