Mr. Sayala ya ce, kasar Sin dake karkashin jagorancin JKS, ta cimma nasara wajen neman bunkasuwar kasa baki daya. Kuma tattalin arziki kasar Sin ya ci gaba da bunkasa cikin sauri, lamarin da ya sa, kasar ta kasance kasa ta biyu wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a nan duniya. Wannan shi ne babbar nasara da kasar ta cimma.
Haka kuma ya nuna cewa, kasar Sin tana maida hankali kan neman daidaito a tsakanin bunkasuwar zamantakewar al'umma da kiyaye muhalli, shi ya sa tana ci gaba da kyautata tsarin neman bunkasuwa, lamarin da ya kasance babban dalilin da ya sa, ake samun ci gaba bisa fannoni daban daban cikin sauri a kasar Sin.
Haka kuma, an yi amanna cewa, kasar za ta ci gaba da cimma nasarori bisa fannoni daban daban a nan gaba, bisa jagoranci na JKS. (Maryam)