in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu shugabannin kasashen duniya sun taya Xi Jinping murnar sake zama babban sakataren JKS
2017-10-30 14:00:30 cri
Kwanan baya, wasu shugabannin kasashen duniya da na jam'iyyun siyasa sun aiko da wasiku, don taya shugaba Xi Jinping murna bisa sake zabensa babban sakataren kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 2.

Cikin sakonsa na murna da shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya mikawa shugaba Xi Jinping, ya ce, a matsayinsa na shugaban jam'iyyar ANC kana shugaban kasa, yana taya Xi Jinping murnar sake zama babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS.

Shi ma shugaban kasar Senegal Macky Sall ya nuna cewa, nasarar da shugaba Xi ya cimma, ya nuna amincewar al'ummomin kasar kan muhimmiyar rawa da ya taka wajen raya tattalin arziki da zaman takewar al'ummar kasa baki daya.

Haka kuma, shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ce, nasarorin da aka cimma a taron wakilan JKS sun nuna goyon bayan da jama'ar kasar Sin suka baiwa shugaba Xi. Kuma, ya yi imani cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki, da zaman takewar al'umma a nan gaba.

A nasa bangare kuma, babban sakataren jam'iyyar MPLA ta kasar Angola Antonio Paulo Kassoma ya ce, an cimma manyan kudurori a yayin taron wakilan JKS karo na 19, wadanda za su kasance jagora ga al'ummomin kasar Sin wajen gina wata kasa mai wadata da samun daidaito. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China