in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar wakilan JKS ta gwamnatin Sin ta kira taro don koyon ka'idojin cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19
2017-10-29 13:28:40 cri
A ranar 26 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ba da jagoranci kan taron kungiyar wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta gwamnatin kasar, domin kara saninsu game da ka'idojin cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19, ta yadda za a gudanar da ayyukan gwamnatin kasar yadda ya kamata a nan gaba.

A yayin taron, an bayyana cewa, a cikakken zaman taron wakilan JKS da aka kammala a ranar 24 ga wata, an bayyana babban alhakin dake wuyan jam'iyyar cikin sabon zamani, yayin da tabbatar da matsayin tsarin gurguzu na kasar Sin cikin tarihin bil Adama. Bisa rahoton da kwamitin tsakiya karo na 18 ya bayar, an nuna babban burin wadata da jama'ar kasa baki daya, da kuma cimma nasarar gina tsarin gurguza a kasar Sin, lamarin da zai ba da jaroranci kan yadda za a gudanar da ayyukan JKS da gwamnatin kasar Sin a nan gaba.

Haka kuma, tsarin gurguzu da ake ginawa karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, ya kasance daya daga cikin muhimman bangarori wajen cimma nasarar aiwatar da tsarin gurguzu a kasar Sin, ya kamata a ci gaba da aiwatar da tsarin cikin himman da kwazo.

Bugu da kari, a yayin taron, an bayyana cewa, ya kamata kungiyar wakilan JKS ta gwamnatin kasar Sin da hukumomin gwamnatin kasar su dukufa wajen koyon ka'idojin cikakken zaman taron JKS karo na 19, domin aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.

A sa'i daya kuma, a kara sani game da muhimman ci gaba da aka samu cikin shekaru 5 da suka gabata a nan kasar Sin, bisa kokarin da aka yi wajen bude kofa ga waje da kuma raya harkokin zamani bisa tsarin gurguzu. Domin yin amfani da su cikin ayyukan da za a yi, da kuma warware matsalolin dake gaban kasar wajen neman bunkasuwa, da kuma cimma burinta na samun dauwamammen ci gaba da kuma kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar Sin baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China