Dmitry Medvedev shi ne shugaban kasar waje na farko da ya kawo ziyara kasar Sin bayan kammala babban taron wakilan JKS na 19, abun da Li Keqiang ya bayyana a matsayin alamu dake nuna dangantaka ta kut-da-kut dake tsakanin Sin da Rasha.
Li Keqiang ya ce a shirye kasar Sin ta ke ta kara hadin kai da aminci da musayar bayanai da Rasha, domin ganin an cimma burin dangantakar ta hanyar amfani da irin ziyarar da Firaministan Rashan ya kawo da kuma sauran matakan hadin gwiwa.
Firaministan na kasar Sin ya kuma yi wa takwaranasa na Rasha bayani game da babban taron wakilan JKS na 19.
A nasa bangaren, Dmitry Medvedev ya taya kasar Sin murnar nasarar babban taron. Ya na mai yabawa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin mai muhimmanci da kyakkywar makoma.
Ya ce Rasha na sa ran ganin hadin gwiwar dake tsakaninta da Sin ya samu dimbin nasarori.
Medvedev na ziyarar aiki a kasar Sin ne daga jiya Talata zuwa gobe Alhamis. A kuma yau Laraba ne Li Keqiang da Dmitry Medvedev za su yi ganawa karo na 22, da aka saba yi tsakanin Firaministocin kasar Sin da Rasha, dake da nufin tabbatar da dorewar huldar dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)