Dan majalisar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi, da sakataren tsaron kasar Rasha Nikolai Patrushev ne suka jagoranci taron tuntubar.
An bayyana taron a matsayin mafi alfanu a tarihin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Yang ya bukaci bangarorin biyu dasu kara zakulo dabarun da zasu tabbatar da samun fahimtar juna da amincewa da juna don yin aiki tare da juna da nufin tabbatar da cigaban sha'anin tsaro, da karfafa sauran al'amurra da suka shafi moriyar kasashen biyu.
A nasa bangaren Patrushev, ya bayyana cewa, karfafa huldar diplomasiyya tsakanin bangarorin biyu shine babban abin da Rashar take dauka da muhimmanci, kana yayi alkawari cewa kasar Rasha zata cigaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin domin tsara dabarun tabbatar da tsaro da ma sauran batutuwa da suka shafi tafiyar da al'amurran kasa da kasa.