Yayin taron, ministan masana'antu da fasahar sadarwa na kasar Sin Miao Wei da ministan masana'antu da cinikayya na Rasha Denis Manturov, sun tattauna kan hadin gwiwa a fannonin da suka hada da sufurin jiragen sama da kayayyakin da ake sarrafawa da kayayyakin aiki da kuma kayan latroni.
Bayan tattaunawar, ministocin biyu sun kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar jarin da kasar Sin za ta zuba a jamhuriyar Tatarstan na Rasha da kuma yarjejeniyar fahimtar juna ta gudanar da gasa kan kirkire-kirkire tsakanin Sin da Rasha.
Kusan wakilai 200 da suka hada da babban wakilin Sin a Kazan da 'yan kasuwa da malamai daga cibiyoyin ilimi na kasashen biyu ne suka halarci taron. (Fa'iza Mustapha)