in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin shugabannin Sin da Rasha
2017-04-14 13:59:50 cri
A jiya Alhamis ne mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Gaoli, wanda ke ziyara a kasar Rasha bisa gayyatar da aka yi masa, ya gana da shugaban kasar Vlładimir Putin a birnin Moscow.

A yayin ganawar, mista Zhang ya yi bayani kan ci gaban da kasashen biyu suka samu a fannonin hadin kan makamashi, da zuba jari, da kuma kudi. Ya kuma jaddada cewa, muhimmin dalilin sa na ziyarar shi ne, waiwaye nasarorin da kasashen biyu suka samu a wadannan fannoni, kana da tattaunawa kan sabbin matakan da ake dauka, da nufin tabbatar da muhimman ra'ayi na bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

Mista Zhang ya kara da cewa, daga ranar 14 zuwa 15 ga watan Mayu, kasar Sin za ta shirya babban taron dandalin tattaunawa na hadin kan kasa da kasa game da shirin "Ziri daya da hanya daya" a birnin Beijing.

Ya ce hada shirin "ziri daya da hanya daya da" kawancen tattalin arziki tsakanin Turai da Asiya, ra'ayi ne na bai daya wanda shugaba Xi Jinping da shugaba Putin suka cimma, kuma a yanzu haka hukumomin da batun ya shafa na kasashen biyu suna gaggauta tabbatar da nasarar hakan.

A nasa bangare, shugaba Putin ya bukaci mista Zhang da ya isar da gaisuwarsa ga shugaba Xi Jinping, ya kuma bayyana cewa, yana farin cikin halartar wancan dandalin tattaunawar bisa gayyatar da shugaba Xi ya yi masa. Ya kara da cewa, yana maraba da mista Zhang, bisa halartar taron tsarin hadin kan kasashen Sin da Rasha. Yana mai fatan cewa, kasashen biyu za su kara habaka fannonin hadin kai a tsakaninsu, don kara inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China