in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin MDD da na AU sun yi kira da a dauki matakan maimaita zaben Kenya cikin lumana
2017-10-23 19:44:14 cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, da shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, sun yi kira da a dauki matakai da za su ba da damar gudanar maimaicin babban zaben kasar Kenya cikin lumana.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da sassan biyu suka fitar, sun ja hankalin jagororin siyasar kasar ta Kenya, da su kaucewa daukar matakai da ka iya rura wutar rikici.

Kaza lika sun bukaci masu ruwa da tsaki a zaben dake tafe ranar 26 ga watan nan, da su hada kai da hukumar zaben kasar Kenya ko IEBC, ta yadda za a samu nasarar kammalar zaben lami lafiya.

Wannan dai kira na zuwa ne, bayan da jagoran tsagin 'yan adawar kasar Raila Odinga ya ayyana kauracewa zaben gaba daya.

A daya hannun kuma, Mr. Guterres da Mahamat, sun bayyana aniyar su ta tallafawa kasar Kenya, wajen tabbatar da gudanar zaben bisa mutunta tanaje tanajen kundin tsarin mulkin kasar.

Mr. Odinga dai ya kalubalanci sakamakon zaben ranar 8 ga watan Agustan da ya gabata, yana mai cewa gwamnatin kasar mai ci, ta tafka magudi domin tabbatar da nasara ga shugaba Kenyatta.

A kuma ranar 1 ga watan Satumba ne kotun kolin kasar ta soke sakamakon da aka ayyana, a wani mataki da ya yi matukar baiwa duniya mamaki.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China