in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Kenya: Ya kamata dukkan 'yan takara su sake shiga zaben shugaban kasar
2017-10-12 11:10:27 cri
Hukumar zaben kasar Kenya da harkokin iyakar kasar ta bayar da sanarwa a daren ranar 11 ga wata cewa, za a sake gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 26 ga wannan wata bisa shirin da aka tsara, dole dukkan 'yan takara 8 su sake halarci zaben.

A watan Agusta na bana, hukumar zaben kasar Kenya da harkokin iyakar kasar ta sanar da shugaban kasar na yanzu Uhuru Kenyatta ya samu zarcewa kan mukamin shugaban kasar. Babban madugun jam'iyyar adawa na kasar Raila Odinga, ya ki amincewa da sakamakon, inda ya garzaya kotun kolin kasar. A ranar 1 ga watan Satumba, kotun kolin kasar ta soke sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar. Hukumar zaben kasar da harkokin iyakar kasar ta sanar da cewa, za a sake yin zaben shugaban kasar a ranar 26 ga watan Oktoba. Amma a ranar 10 ga wannan wata, Odinga ya sanar da kauracewa shiga zaben da za a sake yi, tare da bukatar a sake shirya zaben shugaban kasar a cikin kwanaki 90. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China