Shugaban cibiyar nazarin manufofin kasashen Afirka na kasar Kenya Peter Kagwanja, ya bayyana a kwanan nan cewa, ya kamata Jam'iyyu masu mulki na kasashen Afirka su koyi fasahohin da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta CPC ta samu a fannin mulkin kasa, a kokarin samun wata hanyar ci gaban da ta dace da yanayinsu.
Mr. Kagwanja ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da wakilin sashen Swahili na CRI, inda ya kuma bayyana cewa, yana da imani sosai ga kasar Sin bayan babban taron wakilian Jam'iyyar CPC karo na 19, kuma yana sa rai game da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, kasar Sin mai matukar karfi za ta taimakawa ci gaban Afirka.(Kande Gao)