Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Yusuf ya bayyana a cikin sakonsa cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin gami da jama'ar kasar Sin sun goyi-bayan Xi Jinping don zama babban sakataren jam'iyyar ne, saboda namijin kokarin da ya yi a fannin raya kasa, da jagorantar kasar ta za ta kara samun ci gaba da wadata, abun da ya sa Sin ta samu yabo matuka daga fadin duniya.
A nasa sakon shugaban Jamhuiyar Mali, Ibrahim Boubacar Keita, cewa ya yi, Xi ya sake zama babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta Sin, saboda dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu a yayin da yake jagorancin jam'iyyar. Keita yayi imanin cewa, Xi Jinping zai ci gaba da dukufa kan aikin raya kasar Sin gami da kyautata zaman rayuwar al'ummar kasar a cikin sabon wa'adin aikinsa.
Shi kuma a nasa sakon, shugaban kasar Saliyio, kana jagoran jam'iyyar All People's Congress (APC) Ernest Bai Koroma, ya ce, a madadin gwamnati da jama'ar Saliyo, ya taya Xi Jinping murnar sake zama babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta Sin. Koroma ya kuma nuna matukar godiyarsa ga Xi Jinping, saboda tallafi da taimakon da ya baiwa gwamnati gami da jama'ar kasar Saliyo.(Murtala Zhang)