Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adeshina ya sanyawa hannu, shugaba Buhari ya bayyana tabbacin cewa, kammala babban taron wakilan JKS karo na 19 da muhimman shawarwarin da aka aiwatar, za su kasance jagoran cimma nasarar manufofin raya da mahukuntan kasar ta Sin suka tsara.
Ya ce, hakika kasar Sin ta cimma muhimman nasarori masu tarin yawa a shekaru biyar din da suka gabata, kuma babu tantanma sabbin shugabannin da aka zaba za su ci gaba da kara hada kan JKS ta yadda za ta kai ga cimma nasarar tanade-tanaden raya kasa da aka bijiro da su.
Shugaban na Najeriya ya kuma bayyana tabbacin cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, jagororin JKS da shugaba Xi za su kai kasar Sin zuwa ga sabon tafarki tare da kara daga matsayinta a duniya.
Ya ce, yadda suke yawan tattaunawa da takwaransa na kasar Sin, ya baiwa kasashen biyu damar karfafa alaka a fannonin tattalin arziki da makamashi. Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yaba alakar dake tsakanin kasashen biyu da ma nahiyar Afirka, musamman yadda aka samu dorewar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC).
Daga karshe shugaba Buhari ya yiwa shugaban Xi da ake sake zaba fatan kammala wa'adinsa na biyu cikin nasara. (Ibrahim)