in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda aka sanya "ziri daya da hanya daya" cikin kundin tsarin mulkin JKS zai samar da babban kuzari ga aikin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama
2017-10-26 20:15:27 cri
Taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da aka gudanar a kwanan baya, ya zartas da kudurin shirin gyaran fuska ga tsarin mulkin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda aka sanya shawarar"ziri daya da hanya daya" cikin kundin. Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang a yau Alhamis ya bayyana cewa, matakin zai samar da babban kuzari ga kokarin da kasar Sin ke yi, na hada kai da bangarori daban daban wajen raya "ziri daya da hanya daya", da raya huldar kasa da kasa ta sabon salo, da kuma raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adam.

A gun taron manema labarai da aka kira a wannan rana, kakakin ya ce, yadda aka sanya shawarar "ziri daya da hanya daya" da sauran batutuwa cikin kundin tsarin mulkin jam'iyyar, ya shaida niyyar gwamnatin kasar Sin da ke karkashin shugabancin jam'iyyar, ta hada kan kasa da kasa wajen raya ziri daya da hanya daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China