in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya taya Xi bisa sake zabensa a matsayin babban sakataren CPC
2017-10-26 09:26:53 cri

A jiya ne shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Sin shugaba Xi Jinping, inda ya taya shi murnar sake zabarsa a matsayin babban sakataren kwamitin koli na JKS, da kuma murnar kammala babban taron wakilan JKS karo na 19 cikin nasara.

Shugaba Trump ya ce, taron ya janyo hankalin kasashen duniya, kuma shi kansa ya bibiyi muhimman sakannin da shugaba Xi ya aike a taron.

A game da ziyarar da yake shirin kawo wa kasar Sin kuwa, shugaba Trump ya ce, Amurkawa na tattauna wannan ziyara, yana kuma fatan ganawa da shugaba Xi a birnin Beijing domin yin musayar ra'ayoyi kan yadda za su karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu da ma batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da ke shafarsu.

A nasa martanin, shugaba Xi ya gode da sakon fatan alherin da takwaransa na Amurka ya aiko masa, yana mai cewa, abu mai muhimmanci a taron na CPC karo na 19 da aka kammala shi ne jadawalin raya kasar Sin a nan gaba da taron ya shata.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta bi turbar raya kasa cikin lumana, da aiwatar da manufar zurfafa gyare-gyare a gida da kara bude kofa ga kasashen waje, da samun moriya tare, da kara yin hadin gwiwa da manyan kasashen duniya.

Ya ce, kasar Sin tana dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasahen biyu, kuma tana fatan karfafa wannan alaka bisa akidar mutunta juna da samun moriya tare. Ya kuma fatan ganawa da shugaba Trump yayin ziyarar da zai kawo kasar Sin nan ba da dadewa ba don tattauna muhimman batutuwan da za su kawo alheri ga al'ummomin kasashen duniya, bayar da muhimmiyar gudummawa ga kokarin da ake na samar da zaman lafiya a duniya baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China