Ofishin samar da tallafi na MDD dake Somalia (UNSOM) ya sanar da cewa, mahalarta bitar za su samu kyakkyawar fahimta game da irin rawar da za su taka wajen gudanar da ayyukansu na kare rayuwar fararen hula, da mutane marasa galihu, da wadanda aka mayar da su saniyar ware musamman mata da kananan yara.
Taron bitar wanda ke gudana a Baidoa, dake kudu maso yammacin babban birnin kasar, ya samu halartar rundunar sojin kasar Somaliya SNA, da kuma dakarun 'yan sanda na musamman na kudu maso yammacin kasar Somaliya.
Ministar mata da kare hakkin bil adama ta jihar kudu maso yammacin kasar Somaliya Nadifa Armey Abdullahi, ta bayyana cewa taron bitar zai taimakawa jami'an tsaro wajen samun kyakkyawar fahimtar hakkin bil adama, kasancewa suna ta'ammali da bangarorin al'umma daban daban. (Ahmad Fagam)