Kwamishina mai kula da yankin Kigoma na Tanzania Emmanuel Maganga, ya ce musayar fursunonin ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma, a karshen wani taron makotaka na yini daya da aka yi ranar 29 ga watan Yulin da ya gabata, tsakanin kwamitocin tsaro na yankin Kigoma na Tanzania da na yankunan Makamba da Cankuzo da Rutana da Rumonge da Ruyigi na Burundi.
Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho a jiya, Emmnuel Maganga ya ce yankunan shida, sun kuma amince da yin musayar bayanan sirri tun daga hukumomin gwamnatocin kananan hukumomi har zuwa hukumomi na kasa.
Ya ce tabbas an cimma nasara yayin taron, domin dukkan bangarorin sun amince su yi musayar ra'ayi cikin kyakyyawan yanayi.
Har ila yau, kwamishinan wanda ya jagoranci kwamitin tsaro na yankin Kigoma, ya ce bangarorin sun kuma amince su hada hannu wajen gudanar da ayyukan tare, da nufin magance laifufukan da ake aikatawa a kan iyakokin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)