Cikin wani rahoto wanda kungiyar kula da masu zuba jari ta Zanzibar ZATI, ta kaddamar ya nuna cewa, karancin kwararrun mutane dake tafiyar da al'amurran fannin shi ne babban kalubale dake neman durkusar da ci gaban fannin yawon shakatawa a tekun tsibirin Indiya.
Wannan fannin kasuwancin wanda kasar Tanzaniya ke samar da kudaden gudanarwa, rahoton ya ba da shawara game da yadda za'a inganta shi, tare da samar da kwararrun ma'aikata a yankin na Zanzibar, rahoton ya ce dole a inganta kwarewar 'yan asalin kasar.
Bugu da kari rahoton ya ba da shawarar inganta samar da kwarewa a fannonin ilmi da ba da horon sanin makamar aiki.
Haka zalika, an bukaci samar da wani shirin bada horo na musamman ga ma'aikatan dake aiki a yankin, domin su fahimci yadda za su tafiyar da ayyukansu da kuma ba da fifiko kan irin kwarewar da suka samu. (Ahmad Fagam)