in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da firaminitan kasar Somaliya
2017-09-22 10:56:19 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da firaministan kasar Somaliya Hassan Ali Khaire a jiya Alhamis, yayin da yake halartar babban taron MDD a birnin New York na Amurka.

Cikin ganawar Mr. Khaire ya bayyana cewa, akwai dankon zumunci a tsakanin kasashen Somaliya da Sin, kuma jama'ar kasarsa ba za su taba mantawa da goyon baya da tallafi da kasar Sin ta bai wa Somaliya ba, yayin da take neman samun 'yancin kai da ci gaba.

A nasa bangaren, Wang Yi, ya furta cewa, kasar Sin na mara wa sabuwar gwamnatin Somaliya baya, wajen jagorantar jama'ar kasar don samun ci gaba cikin lumana. Kana Sin na da niyyar hada gwiwa da Somaliya a fannoni daban-daban ta hanyar raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da bin tsarin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka na FOCAC, da tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China