in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Togo sun soki tarzomar kin jinin karin kudin mai
2017-03-01 20:00:00 cri

Mahukunta a kasar Togo sun yi Allah wadai da barkewar wata tarzoma, wadda ta yi sanadiyyar rasuwar mutum guda, tare da jikkatar wasu 'yan sanda da dama, biyowa bayan karin kudin man fetur da kalanzir da aka yi a kasar.

Cikin wani sako da gwamnatin kasar ta gabatar ta kafofin talabijin, an yi suka game da tashin hankali da ya barke a daren jiya Talata, bayan ayyana fara aiki da sabon farashin man fetur da kalanzir din, tun daga jiyan wato 28 ga watan Fabarairu.

Sanarwar ta ce karin da aka samu ya biyo bayan karyewar da farashin gurbataccen mai ke yi ne a kasuwar duniya, da kuma karuwar farashin dala. Kaza lika gwamnatin Togo ta ce a baya, gwamnatin kasar ta sha rage farashin albarkatun mai domin samar da sauki ga 'yan kasar, kuma a nan gaba ma za ta ci gaba da bada tallafi, domin rage tsadar sa ga al'ummar kasar.

Daga nan sai sanarwar ta jaddada sukar zanga zangar da ta auku, da ma abun da ya biyo bayan ta na barnata dukiyoyi, da kuma jikkata wasu jami'an tsaro, tana mai kira ga al'ummar kasar da su kai zuciya nesa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China