Madam Legzim-Balouki ta yi furucin a yayin bikin ranar masana'antu ta Afrika da aka gudanar a ranar 20 ga watan Nuwamba bisa taken wannan shekara "zuba jari na shekaru goma na uku na cigaban masanasa'antu domin Afrika: Kalubaloli da dabarun samun moriya". Ministar ta tunatar cewa dandalin masana'antu na kungiyar ECOWAS, da aka gudanar a birnin Accra na kasar Ghana a ranar 21 ga watan Yuli ya bukaci kasashe mambobi na gamayyar dasu karfafa asusun musammun na ajiya domin kara halartar shiyyar ga musanyar kayayyakin da ake kerawa a duniya.
Game da wannan, ta nuna yabo ga shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe, wanda bai jira ba domin yin kira da a kafa wata cibiyar kasa ta bunkasa da tabbatar da ajiyar zuba jari domin musammun ma bunkasa kananan masana'antu da matsakaita (PME/PMI) domin matasa. (Maman Ada)