in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Togo za ta karbi bakuncin taron WAHO
2016-12-19 10:15:45 cri
Rahotanni daga kasar Togo na cewa, kasar ta shirya tsaf don karbar bakuncin taron kungiyar masana magungunan gargajiya da na zamani na kasashen yammacin Afirka (WAHO) karo na 8.

Manufar wannan taro wanda zai gudana a birnin Lome, daga ranar 19 zuwa 20 ga wannan wata, ita ce zurfafa hadin gwiwa tsakanin masana magungunan gargajiya da na zamani da ke kasashe 15 na kungiyar ECOWAS, ta yadda za a fito da magungunan da za su kai warkar da sabbin cututtukan da ke gallabar al'umma.

A jawabinsa jami'in kungiyar WAHO da ke Togo Sossah Remi ya bayyana cewa, ana kuma sa ran mahalarta taron za su tattauna kan yadda ilimin harhada magungunan gargajiya zai kara samun karbuwa a duniya, amfani da magunguan gargajiya wajen warkar da cututtukan da aka yi watsi da su a kasashe masu zafi, da binciken yadda za a bunkasa magungunan gargajiya, 'yancin mallakar fasaha da kiyaye fasahohin masana a wannan fanni.

Kungiyar WAHO ta ce, yanzu haka tsarin tafiyar da harkokin kiwon lafiya a sassa daban-daban na duniya ya canja tun bayan da aka gano magungunan zamani da kuma yadda ake samar da su fiye da kima sama da shekaru 100 da suka gabata.

Taron na wannan karo yana zuwa ne a dai-dai lokacin da galibin al'ummar da ke yammacin Afirka ke raja'a ga magungunan gargajiya wajen warkar da kanana da manyan cututtuka kamar na zuciya da jijiyoyin, hawan jina da makamantansu. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China