Dramani ya bayyana cewa, Togo da Sin suna da dadadden tarihi na sada zumunta, Togo ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kana tana fatan hada kai tare da kasar Sin, ta yadda za a samun sabon sakamako a hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannoni daban daban.
A nata bangare, Xu Lvping ta bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin tana son hada kai tare da jam'iyyar Rally for the Republic, ta yadda za a aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito, da sa kaimi ga bunkasa hadin gwiwarsu.
A yayin ziyararta, Xu Lvping ta yi shawarwari tare da shugabannin jam'iyyar Rally for the Republic dake kasar. (Zainab)