in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministar cinikin kasar Togo ta nuna damuwa game da rashin aiki da dokar bunkasa Afrika
2017-08-09 13:45:03 cri
Ministar kasuwanci ta kasar Togo ta bayyana cewa, dokar da Amurka ta kafa don samar da damammaki da cigaban Afrika wato AGOA, bata yin tasiri ga cigaban tattalin arzikin kasashen Afrika.

Bernadette Legzim-Balouki, ministar ciniki da bunkasar kamfanoni masu zaman kansu ta kasar Togo, ta bayyana hakan ne a lokacin taron dandalin kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin al'umma karo na 16, wanda aka gudanar a Lome, babban birnin kasar Togon.

Ministar ta bayyana rashin amfani da dokokin na AGOA da cewa su ne manyann kalubaloli dake haifar da koma baya game da sha'anin gudanar da al'amurran kudade da kasuwanci a nahiyar ta Afrika.

Ta ce dole ne a magance wadannan kalubalolin idan ana bukatar tabbatar da samun gogayya tsakanin kamfanonin nahiyar Afrika ta yadda kayayyakin da suke samarwa za su iya yin gogayya da takwarorinsu na kasa da kasa a kasuwannin duniya, musamman wajen samun karbuwa a kasuwannin Amurka.

Legzim-Balouki ta ce, taron dandalin na Lome ya ba da dukkan damammaki yadda za'a tattauna da kuma bada gudunmowa game da yadda za'a bunkasa harkokin cinikayya tsakanin Amurka da kasashen da ke kudu da hamadar saharar Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China