Kwamitin tsaron MDDr ya bukaci gwamnatin kasar Mali da ta hanzarta bankado wadanda suke da hannu wajen kaddamar da harin, kuma ta gaggauta gurfanar dasu a gaban kotu.
Kwamitin tsaron MDDr ya bayyana harin da aka kaddamar kan jami'an wanzar da zaman lafiyar da cewa zai iya zama laifukan yaki ne karkashin dokokin kasa da kasa.
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, yayi Allah wadai da kaddamar da harin kan sansanin dakarun kiyaye zaman lafiyar a Mali.