Guterres wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya kuma bayyana kudurin MDD na ci gaba da taimakon gwamnati da al'ummar kasar Mali da kungiyoyi masu dauke da makamai da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar kasar, a kokarin da suke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, ta hanyar yakar ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.
Bugu da kari, Guterres ya aike da sakon ta'aziya ga gwamnati da iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar wannan hali, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.(Ibrahim)