in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 9 ne suka mutu sakamakon harin ta'addanci a wurin yawon shakatawa a Mali
2017-06-20 13:38:00 cri
A jiya Litinin 19 ga watan nan ne ministan tsaron kasar Mali Salif Traore, ya tabbatar da cewa, mutane 9 sun mutu sakamakon harin ta'addanci da aka kai a wani wurin taruwar 'yan yawon shakatawa dake gabashin karkarar birnin Bamako, fadar mulkin kasar Mali da yammacin Lahadi 18 ga wata.

Minista Salif Traore ya bayyana cewa, baki daya 'yan yawon shakatawa 4 da soja daya, da kuma 'yan ta'adda 4 sun mutu a sakamakon aukuwar wannan lamari.

A jiya Litinin 19 ga wata, kungiyar masu tsattsauran ra'ayin islama dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda, ta yi shelar daukar alhakin tsarawa tare kuma da gudanar da wannan danyen aiki a wata tashar yanar gizo.

An dai kafa wannan kungiya ce a watan Maris na shekarar bana. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China