in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi Allah wadai da harin da aka kai Mali
2017-06-20 09:38:45 cri
Shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka(AU) Moussa Faki Mahamat ya yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da harin ta'addancin da aka kaiwa jami'an tsaro da fararen hula a wurin shakatawa na Le Campement Kangaba dake gabashin birnin Bamako, babban birnin kasar

Da yake bayani cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, Faki ya sake nanata kudurin kungiyar na ci gaba da baiwa gwamnati da al'ummar kasar goyon baya a kokarin ganin an yaki ayyukan ta'addanci tare da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar.

Shugaban ya kuma mika sakon ta'aziyar kungiyar ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar harin, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Ya kuma bayyana cewa, kwamitin tsaron MDD yana duba yiwuwar amsa bukatar da kasashe biyar na yankin Sahel suka gabatar masa.

Harin na jiya da dare dai na zuwa ne mako guda bayan da kasashe hudu dake yankin na Sahel suka bukaci kasashen duniya da su agazawa yarjejeniyar hadin gwiwar kasashen biyar dake yankin Sahel ta yadda za su magance matsalar tsaro a kan iyakokinsu, ciki har da batun ayyukan ta'addanci, munanan laifuka da fadan kabilanci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China